Insane
Sulaiman20Ibn20Hujjah 2
Barka20Da20Zuwa
Shafi20Mai20Albarka



¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

Zaka iya kiran wayata tanan
HomeBlogAbout MeBayani Akan AZUMIAikin Hajji da UmaraMa anar Shi aAbin da Aka HanaSamun FalalaKasuwanci Mai RibaMahimmancin Addu o iBayanin ZakkaSALLAMATA A MUSULUNCITSARKITAUHEEDI DA AQIDAAYYUKAN ZUCIYAMAHIMMANCIN DA AWATAMBAYA DA AMSASheikh jafar mahmud AdamWadansu websides


SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH


Sheik Lawan Abubakar Gadon Kaya tafseer2017



02/05/24
FB Pantami


Ibn20Hujjah
Source: Google news
0Mozilla/5.0




SULAIMAN Ibn Hujjah

* No categories

Online: Guests: 1


Sulaiman20 FaceBook


AZUMI
Azumin watan Ramadan ya wajaba akan kowane musulmi, mai hankali, baligi wanda zai iya yin azumi ban da mai haila ko jinin haihuwa.
Kuma ana yiwa yaro umarni da shi idan zai iya domin ya saba.
Kuma a na samun shigar watan Ramadan da dayan abubuwa biyu:
(1)Ganin jinjirin wata da shaidar musulmai adali wanda hukunci ya hau kansa, ko da mace ce.
(2)Cikar watan sha'aban kwanaki talatin, kuma wajibcinsa yana farawa daga bullowar alfijir na gaskiya zuwa faduwar rana.
Kuma babu makawa a zumin farilla sai an yi niyyarsa kafin alfijir.

**ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI**
(1) Yin jima'i ta cikin farji: kuma dole a yi ramuwa da kaffara. kaffara ita ce: 'yanta bawa, wanda kuma bai samu ba, sai yayi azumin wata biyu a jere. Wanda ya kasa sai ya ciyar da miskinai sittin, to wanda bai samu ba babu komai a agare shi.
(2) Fitar da maniyyi: saboda dalilin sumbanta ko shafa ko istimna'i. Amma babu komai akan wanda yayi mafarki.
(3) Ci ko sha da gangan, idan da mantuwa ne to azuminsa ya inganta.
(4) Fitar da jini ta hanyar kaho ko bayar da jini domin agaji, amma fitar kadan ta wurin (awo)ko abinda yake fita ba tare da nufi ba kamar jinin ciwo ko habo to baya bata azumi.
(5) Yin amai da gangan.
Idan wata kura ta shige ta cikin makogwaro, ko ya kurkuri baki ko ya shaki ruwa sai ruwa ya isa makogwansa, ko kuma ya yi tunani har ya fitar da maniyyi ko yayi mafarki, ko wani jini ya fito masa ko amai ba tare da yayi nufi ba, to bai bata azumin sa ba.

Wanda yaci abinci yana zaton dare ne sai ya bayyana masa (ya gane) cewa rana ne, to zai rama. Wanda yaci da daddare yana mai shakkar bullowar alfijir to bai bata azuminsa ba.
kuma idan yaci da rana yana shakkar faduwar rana to zai yi ramuwa.

**HUKUNCE -HUKUNCEN WADANDA SUKE AJE AZUMI**
Yana haramta ajiye azumi ga wanda ba shi da wani uzuri da Ramadan.
Kuma ya wajaba mai haila ta ajiye azumi, ko mai jinin haihuwa, da kuma wanda yake da bukatuwar kubuta daga halaka.
Kuma sunna ce ga matafiyin da ta kai yin kasaru ya ajiye idan ya yi masa wahala, ko mara lafiya da yake gudun cutuwa.
Kuma ya halatta wanda zai yi tafiya da rana ya ajiye. ko mai ciki ko mai shayarwa saboda tsoron kansu ko yaransu.
Dukkan wadannan ramuwa ne kawai a kansu.
kuma mai ciki ko shayarwa zata yi kari da ciyar da miskini ko wace rana idan tsoron da taji ga yara ne kawai.
Wanda ya kasa azumi saboda tsufa ko ciwo wanda ba a tunanin warkewa to kullum sai ya rika ciyar da miskini daya kuma babu ramuwa a kansa.

Wanda kuma ya jinkirta ramuwa saboda wani uzuri har wani Ramadan din ya same shi zai yi ramuwa kawai.
Idan kuma ya kasance ba tare da uzuri ba ne, zai ciyar tare da ramuwan kowane yini.
Idan ya bar ramuwa saboda wani uzuri sai ya mutu, to babu komai a kansa.
Idan ba tare da uzuri ba ne sai a ciyar masa da miskini na kowane yini, kuma sunna ce ga 'yan uwansa su rama masa abin da ya kubuce masa bai rama ba na Ramadan, da azumin da yayi alwashinsa, da kuma biya masa dukkan wani alwashin da'a da yayi (na sadaka ne ko waninsa).

Wanda kuma ya karya azumi saboda wani uzuri, sannan sai dalilin sa ya gushe da ranar Ramadan to dole ne ya kame.
Haka kuma idan kafiri ya musulunta, ko mai haila tayi tsarki ko mara lafiya idan ya warke, ko matafiyi idan ya iso gida, ko yaro idan ya balaga, ko mahaukaci idan yayi hankali to dole suma su rama (wannan yinin ) koda kuwa sun azumci sashinsa.
baya halatta ga mutumin da bai dau azumin wani yini ba (a cikin Ramadan) saboda wani uzuri na shari'a baya halatta masa ya azumi waninsa a cikinsa (wato watan).

**AZUMIN NAFILA**
Wanda yafi falala shine:- Yin azumi kwana daya, da shan ruwa kwana daya.
Sannan azumin Litinin da Alhamis, sanna azumin kwanaki uku na ko wane wata, kuma yafi kyau a ranakun tsakiyar wata sune (13 da 14 da 15) daga ko wane watan sama.
Kuma sunna ce a azumci yawancin kwanakin watanni Almuharram da kuma Sha'aban' da ranar Ashura, da ranar Arfa, da kwanaki shidda na watan Shawwal.
Kuma an kyamaci ware Rajab, da ranar Jumma'a da Asabar da azumi.
da azumin ranar shakka wadda shi ne ranar talatin ga Sha'aban idan sararin sama ba gajimare a cikinsa.
Haramun ne kuma yin azumi rana salla karama, ko babba (sallan azumi da layya). da ranakun shanya (wato tashrik, ranar sha daya, sha biyu da sha uku na watan babbar sallah) sai dai ga wanda zai yi azumi saboda gagara da ya yi wajen yanka ga hajjinsa na tamattu'i ko kirani.

**ABUBUWAN LURA GAME DA AZUMI**
* Wanda yake da babbar hadasi akansa kamar janaba ko haila ko nifasi idan sun tsarkaka kafin alfijir, to ya halatta su jinkirta wanka har bayan kiran sallar alfijir, su kuma gabatar da sahur, azuminsu kuma yayi.
* Ya kuma halatta mace ta sha magani saboda ta jinkirta haitarta da Ramadan saboda nufin tarayya da musulmi wurin yin biyayyarsu idan babu cutarwa ga lafiyanta.
* Ya kuma halatta ga mai azumi ya hadiye miyau ko majina idan ya kasance daga cikin makogwaro ne.
* Annabi (s a w) yace: "Al 'ummata bata gushewa da alheri matukar sun gaggauta bude baki, sun kuma jinkirta sahur"
kuma yace: "Addini bai gushe ba yana bayyana matukar a na gaggauta buda baki domin Yahudu da Nasara suna jinkirta shi".

* Kuma anso ayi addu'a a wurin buda baki, Manzon Allah (s a w) yace: "Lallai ga mai azumi a wurin buda bakinsa akwai wata addu'a da ba a mayar da ita".
kuma daga cikin abin da yazo daga Annabi (s a w) na addu'oi lokacin buda baki akwai fadarsa mai tsira da aminci:
ZAHABAZ ZAMA'U WABTALLATIL URUKU, WA THABATAL AJRU IN SHA ALLAH
Ma'anarsa: kishirwa ta tafi jijiyoyi sun jike, lada kuma ya tabbata da iznin Allah "
* Kuma sunna ne mai azumi yayi buda baki da danyen dabino, idan bai samu ba sai yaci busasshe. idan bai samu ba sai yasha ruwa.
* Ana so mai azumi ya nisanci kwalli, ko magani a ido ko kunne a lokacin azumi, saboda kaucewa kokwanto.
Idan kuma ya kasance ana bukatarsa to babu laifi ko da ya isa makoshi, azuminsa kuma ya yi.
* Sunna ne yin asuwaki a kowane lokacin azumi ba tare da ki ba a bisa ra'ayi ingantacce.

* Ya kamata a kan mai azumi ya guji yin giba (gulma) ko karya ko makamantansu.
kuma ko da wani ya zage shi sai yace: (ni ina azumi), kuma ta wurin kiyaye harshensa da sauran gabobinsa daga sabo zai kiyaye harshensa.
saboda ya zo daga gare shi (s a w) lallai yace: "Wanda bai bar shaidar zur ba, ko yin aiki da ita to Allah ba shi da bukatar ya ajiye abincinsa ko abin shansa".

SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH A SAUKAKE
* Kuma sunna ne ga wanda aka kira cin abincin, alhali yana azumi to yayi wa mai abincin addu'a, idan kuma baya azumi ya kamata yaci.
* Daren Lailatul-kadri shine mafificin dare a cikin shekara, kuma an kebance samunsa a kwanaki goma na karshen watan Ramadan.
kuma mafi karfin zaton samun daren shine daren ashirin da bakwai, kuma yin aikin kwarai a cikinsa yafi alheri fiye da watanni dubu.
Daren yana da alamomi; daga ciki akwai: Bullar rana safiyar daren da ake tsammanisa, ba tsananin zafi a cikinta, da kuma daidaituwar al'amura kamar saututtukan jakai ko karnuka, kuma musulmi zai iya riskanta ba tare da sani ba.
Abin da ake nema daga gare shi, shine ya dage da ibada a cikin Ramadan kuma musamman ranakun goma na karshe, kuma ana kwaidaitarwa da kar a bar wani dare ya kubuce ba tare da anyi ibada a cikinsa ba.
Idan yayi sallar tarawihi a cikin jama'a to kar ya tashi sai liman ya cika sallarsa domin a rubuta masa ladan tsayuwar daren.

* Wanda ya shiga cikin yinin azumin nafila sunna ce ya cika shi amma ba wajibi ba ne. idan kuma ya bata shi da gangan to babu laifi kuma ramuwa.
**ITIKAFI**
Shi ne mutum musulmi mai hankali ya lazimci masallaci saboda biyayya, kuma sharadi ne mai ittikafi ya zamo ya tsarkaka daga babbar kazanta, kuma mai itikafi ba zai fita ba sai da dalilin da babu makawar fita daga gare shi.
Kamar abinci ko biyan bukata ko wanka na wajibi misali. Kuma yana baci da fita ba tare da dalili ba, haka kuma saduwa (shima yana karya shi).
Kuma sunna ne ayi shi ba a ba a ramadan ba, amma sunnar ta fi karfi a Ramadan, mafi karfi goman karshe, kuma mafi karancin ittikafi sa'a.
An so kuma kar ya gaza kwana da yini. kuma mace ba ta yin ittikafi da izinin mijinta, kuma sunna ne mai ittikafi ya shagaltu da ibada da da'a, Ya kuma bar yawa yawan ayyukan da suka halatta a gare shi. kuma ya nisanci abin da ba ruwan shi

WANNAN SHINE BAYANIN AZUMI

Sulaiman Ibn Hujjah
02/05/2400:34

Sulaiman20Ibn20Hujjah-1 1